Kofin Zakarun Turai: Kila kungiyoyin Ingila 5 su je mataki na gaba

'Yan wasan Liverpool Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Liverpool ta barar da damarta ta farko ta zuwa matakin na gaba a wasan da ta bari Sevilla suka rama cinsu aka tashi 3-3 a baya

Kungiyoyin Ingila guda biyar za su je matakin 'yan 16 na gasar zakarun Turai, a karon farko idan Manchester United da Liverpool suka dace a makon nan.

Tuni sauran kungiyoyin na Ingila da ke gasar, Chelsea da Tottenham da kuma Manchester City suka kai matakin na sili-daya-kwale, duk da wasa daya da ya rage musu.

Man United za ta tsallake zuwa matakin na gaba idan har Basel ta kasa doke Benfica, kuma a hakan ma sai kungiyar ta Jose Mourinho ta sha kashi a gidanta da CSKA Moscow da kwallo fiye da shida a ranar Talata.

A ranar Laraba kuma Liverpool za ta yi nasarar zuwa matakin na 'yan 16, a matsayin ta daya a rukuninta idan ta doke Spartak Moscow a Anfield, a wasansu na karshe, kuma ko da canjaras suka yi Liverpool din za ta tsallake.

Kungiyoyin da suka zama na daya a rukuninsu za a hada da wadanda suka zo na biyu a zagayen na kungiyoyi 16, kuma ba wata kungiya da za a hada ta da wadda suka fito daga kasa ko rukuni daya, yayin da su kuma kungiyoyin da suka kare a matsayi na uku za a tura su gasar kofin Europa.

Tuni Tottenham da Manchester City suka samu matsayi na daya a rukunansu, amma Chelsea ma za ta samu hakan idan ta yi nasara a kan Atletico Madrid ranar Talata.

Daga cikin wasannin na gasar ta zakarun Turai da za a yi ranar Talata akwai:

Bayern Munich da PSG

Barcelona da Sporting CP

Celtic da Anderlecht

Roma da Qarabag

Olympiakos Piraeus da Juventus.

Ranar Laraba kuma za a yi sauran guda takwas.