David Luiz ba zai yi wasa ba - Conte

Antonio Conte (hagu) na gaisawa da David Luiz Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Antonio Conte (a hagu) ya ce David Luiz (a dama), wanda sau daya ya yi wasa a karawar Chelsea shida ta karshe, har yanzu yana fama da ciwon guiwa

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce David Luiz ba zai buga wasansu na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai ba na rukuninsu na uku (Group C), wanda za su yi a gida da Atletico Madrid saboda ciwon guiwa.

Kocin ya kafe cewa rashin sa dan wasan na Brazil a cikin wadanda za su yi karawar saboda sabanin da suka samu ne a tsakaninsu.

Sau daya Luiz, mai shekara 30, ya yi wasa tun lokacin da ya soki kocin nasa a kan salon wasan da ya tsara musu, wanda Roma ta doke su a watan Oktoba.

Conte ya sheda wa manema labarai cewa kungiyar na kokarin shawo kan matsalar raunin guiwar dan wasan, kuma nan da nan ya ce zai yi amfani da dan wasan idan ya samu lafiya.

Chelsea, wadda ta samu zuwa mataki na gaba na gasar zakarun Turai, zagayen kungiyoyi 16, bayan da ta yi nasara a kan Qarabag a watan da ya wuce, za ta zama ta daya a rukunin idan ta yi nasara a kan Atletico Madrid, a Stamford Bridge.

Ita kuwa Atletico dole ne ta yi nasara a kan Chelsea, sannan kuma ta yi fatan Qarabag ta ci Roma a Italiya kafin ta tsallake zuwa matakin na gaba.