West Ham da Sporting Lisbon sun sasanta a kan Carvalho

William Carvalho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption William Carvalho ya fara yi wa Portugal wasa a 2013 kuma yana daga cikin 'yan wasan da kasar ta dauki kofin Turai na 2016

West Ham ta ce rikicin da aka samu tsakaninta da Sporting Lisbon a kan dan wasan da suke son zawarci a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta gaba William Carvalho na Portugal ya faru ne saboda matsalar sadarwa kuma an sansanta ta.

A da kungiyar ta Sporting ta ce za ta kai karar West Ham gaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, saboda zawarcin dan wasan nata na tsakiya mai shekara 25, ba bisa ka'ida ba.

A wata sanarwa da kungiyar ta West Ham ta fitar ta ce kungiyoyin biyu za su dawo su ci gaba da dangantakarsu kamar da.

A watan Satumba West Ham ta ce ta nemi sayen dan wasan na Portugal har ma ta fitar da wasu wasiku na e-mail da take ikirarin cewa ta yi zawarcin dan wasan bisa ka'ida.

Amma kuma darektan sadarwa na Sporting Nuno Saraiva ya kalubalanci ingancin wasikun da e-mail da aka yi satar fitarwa, wadanda suka nuna tayin euro miliyan 25 da aka yi a kan dan wasan.

Darektan ya kuma nuna bayyana Sullivan a matsayin makaryaci kuma cimazaune a wani sako da ya sanya a Facebook.

A lokacin West Ham ta karyata maganganun har ma tana barazanar daukar matakin shari'a.

Sai dai duka bayan wannan musayar kalamai a ranar Talatar nan kungiyar ta Premier ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki take cewa, an samu wannan rashin fahimta ne saboda matsalar sadarwa tsakanin wakilan kungiyoyin biyu, a kan batun zawarcin dan wasan na Sporting, William Carvalho.