Abubuwan kara Kuzari: An haramta wa Rasha zuwa gasar Olympic ta 2018

Shugaban IOC Thomas Bach Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Shugaban hukumar Olympic, IOC, Thomas Bach ne ya sanar da hukuncin a ranar Talata

Hukumar wasannin Olympic ta duniya ta haramta wa Rasha shiga gasar Olympics ta lokacin huturu da za a yi a shekara mai zuwa a Koriya ta Kudu, bayan samunta da laifin hannu a ba wa 'yan wasan kasar abubuwan kara kuzari.

Sai dai hukumar ta ce 'yan wasan kasar wadanda ba a same su da laifin amfani da abubuwan kara kuzari ba za su iya shiga gasar amma ba da sunan kasar tasu ba, sai dai karkashin tutar gasar ta Olympic.

Binciken da aka yi na tsawon wata 17, ya gano shedun da ke nuna tarin zambar amfani da abubuwan kara kuzari da 'yan wasan kasar suka yi a lokacin gasar Olympic ta huturu ta Sochi, wadda Rashar ta karbi bakunci.

Sai dai kuma hukumomin kasar ta Rasha sun musunta duk wani zargi da ake musu a kan lamarin, da cewa sam-sam ba wani abu makamancin haka da kasar ta yi.

Kawo yanzu ba a san ko Rashar za ta bar 'yan wasan nata da ba su da laifin su shiga gasar a matsayin ba 'yan wata kasa ba, ko kuma za ta kaurace wa gasar ta Olympic ta 2018.