Zakarun Turai: Bayern Munich ta doke PSG 3-1

'Yan Bayern na murnar zura kwallo a raga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bayern ta kammala wasannin rukuninta da cin duka karawarta ta gida

Dan wasan tsakiya na Faransa Corentin Tolisso ya daga ragar PSG sau biyu Bayern Munich ta yi nasarar doke PSG 3-1, amma kuma 'yan Faransan sun kai matakin 'yan 16 a matsayin na daya a rukuninsu na gasar zakarun Turai.

Bayern na bukatar ta doke zakarun Faransan da kwallo hudu kafin ta zama ta daya a rukunin na biyu, (Group B).

Robert Lewandowski ne ya fara ci wa zakarun na Jamus bayan minti takwas da shiga fili, sai kuma Tolisso ya biyo baya da ta biyua a minti na 37 da kuma ta uku a minti na 69.

To amma kafin Tolisso ya ci ta uku, bayan ya zura ta biyu, ana 2-0 Kylian Mbappe ya ci wa bakin bal dinsu daya tilo a minti na 50.

A ranar Litinin mai zuwa ne za a hada jadawalin wasannin gaba na gasar ta zakarun Turai a hedikwatar hukumar kwalllon kafa ta Turai Uefa a birnin Nyon na Switzerland.

A rukuni na biyu (Group B) kuwa Celtic ta kammala wasanninta na rukuni a matsayin ta uku, kuma ta samu damar zuwa gasar Europa duk da rashin nasarar da ta yi a gidanta a hannun Anderlecht 1-0.