Kofin Turai: Chelsea za ta hadu da Barcelona ko PSG

'Yan Atletico na murnar zura kwallo a ragar Chelsea Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau uku kawai Atletico suka kai wa Chelsea hari, amma kuma sun fusata masu masaukin nasu

Chelsea na fuskantar yuwuwar haduwa da Barcelona ko Paris St-Germain a wasansu na gaba na kungiyoyi 16 na zakarun Turai bayan suka tashi 1-1 da Atletico Madrid, suka rasa damar zama na daya a rukuninsu.

A yanayin yadda sauran wasannin suka kasance kungiyar Besiktas ta Turkiyya ita kadai ce bayan bayan Barcelona da Atletico Madrid, za a hada Chelsean da ita a matakin na gaba na kwab daya.

Chelsea ce ta mamaye wasan har zuwa lokacin da Saul Niguez ya faki dan bayanta Tiemoue Bakayoko, ya zura musu kwallo da ka, bayan da Fernando Torres ya cillo masa ita a minti na 56.

Chelsea ta kara matsa lamba ba kakkautawa yayin da lokaci ke kurewa, har ta yi sa'a Stefan Savic ya ci kansu da bal din da Eden Hazard ya dauko.

To sai dai Roma a gidanta ta doke Qarabag, kuma Chelsean ta kasa kara cin ta biyu, ta samu nasarar da za ta sa ta sake zama ta daya a rukuninsu na uku (Group C).

Spartak Moscow ko Sevilla wata daga cikinsu ma za ta iya zama wadda za a hada su da Chelsean idan wasan ranar Laraba ya sauya matsayin kungiyoyin rukuni na biyar (Group E), inda Liverpool take ta daya.

Sauran Wasannin na Talata;

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona ta zama ta daya a rukuninsu da maki 14 , bambancin uku da mai bi mata baya Juventus

Barcelona ta doke Sporting Lisbon 2-0, nasarar da ta sa ta zama ta daya a rukuninsu na hudu (Group D), kuma ta kawo karshen fatan Sporting na zuwa gaba a gasar.

Sporting na bukatar ta yi nasara ne sannan kuma Juventus ta yi rashin nasara a gidan Olympiakos, to amma sai zakarun na Italiya suka yi nasara zama na biyu sakamakon cin da suka yi wa masu masaukin nasu 2-0 a Girka.

Benfica 0 -2 FC Basel