Tennis: Johanna Konta ta nada Michael Joyce kociya

Michael Joyce da Maria Sharapova Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Michael Joyce ya taimaka wa Maria Sharapova ta ci manyan kofi biyu

Gwanar tennis ta daya a Birtaniya Johanna Konta ta tabbatar da nadin Michael Joyce, tsohon kociyan Maria Sharapova a matsayin sabon mai horar da ita.

Daman tun a watan Nuwamba BBC ta ruwaito cewa ana tattaunawa domin ba wa kociyan dan Amurka mai shekara 44 aikin.

Joyce ya kai matsayin gwani na 64 a duniya lokacin yana wasan na tennis, sanna ya yi shekara shida a cikin tawagar masu horar da Maria Sharapova, kuma ya yi aiki da Victoria Azarenka a shekarar nan ta 2017.

Konta wadda rabonta da wasa ton watan Oktoba saboda raunin da ta ji a kafarta, ta kai har matsayi na hudu a duniya a wannan shekarar.

'Yar tennis din ta Birtaniya ta kai wasan kusa da karshe na gasar Wimbledon sannan ta dauki kofin gasar Miami Open a shekarar nan, lokacin tana tare da kociyanta dan Belgium Wim Fissette.

Sun raba gari da kociyan ne bayan da kiris ta kuskure samun gurbi a gasar hukumar tennis ta duniya a Singapore, saboda rashin nasara da ta yi sau biyar.

Gasar da za ta yi ta farko da sabon kociyan nata Joyce, ita ce ta Brisbane International, a Australia, wadda za a fara ranar 31 ga watan nan na Disamba.

Sharapova ta dauki kofin gasar Amurka ta US Open da kuma ta Australia sannan kuma ta zama gwana ta daya a duniya a lokacin da Joyce yake mata kociya.