Zakarun Turai: Shakhtar Donetsk ta taka wa Manchester City birki da 2-1

Shakhtar Donetsk lokacin da ta zura kwallo a ragar Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shakhtar Donetsk za ta iya haduwa da Manchester United ko Liverpool ko Tottenham a wasan zagaye na biyu na gasar ta zakarun Turai

Manchester City ta yi rashin nasara a karon farko a wasa 29 yayin da Shakhtar Donetsk ta Ukrain ta doke su da ci 2-1 ta bi City din zuwa matakin wasa na gaba na zakarun Turai.

Man City wadda daman tuni ta zama ta daya a rukuninsu na shida (Group F), ta fara shan kashi ne lokacin da dan Brazil Bernard ya kwararo bal tun daga tazarar yadi 15, ta yi wa golan City Ederson tamkar gaya wa jini na wuce a minti na 26.

Shakhtar ta sake daga ragar Manchester City ta cikin ruwan sanyi ta hannun dan wasanta Ismaily bayan da Ederson ya yi wata kasassaba.

Jagorar ta Premier ta samu dayarta tilo da bugun fanareti a cikin karin lokaci na bayan minti 90, inda Sergio Aguero ya ci, sakamakon ketar da Bohdan Butko ya yi wa Gabriel Jesus.

City ta yi fatan zama kungiyar Birtaniya ta farko da ta yi nasara a dukkanin wasanninta shida na rukuni na gasar zakarun Turai a kaka daya, amma a maimakon haka sai ta gamu da rashin nasararta a karon farko tun bayan da Arsenal ta doke ta 2-1 a wasan kusa da karshe na kofin FA ranar 23 ga watan Afrilu.

A ranar Lahadi 10 ga Disamba, Manchester City za ta je gidan Manchester United (5:30 na yamma agogon Najeriya), sannan kuma ta kara zuwa gidan Swansea City ranar Laraba 13 ga Disamba (8:45 na dare agogon Najeriya). A watan Fabrairu ne za a sake dawowa fagen wasan na kofin zakarun Turai.