Ronaldo ya sake kafa sabon tarihi

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A bana kwallo biyu kawai Cristiano Ronaldo ya ci a La Liga amma yana da tara a gasar zakarun Turai

Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya zama dan kwallo na farko da ya ci wa kungiyarsa bal a dukkanin wasanninta na rukuni a gasar zakarun Turai a kaka daya, inda suka doke Borussia Dortmund 3-2.

Ronaldo ya daga raga ne a minti na 12, da cin da ya zamar masa na tara a gasar ta zakarun Turai ta bana.

Da hakan yanzu ya ci kwallo 114 a gasar zakarun Turai, kuma ya ba wa abokin hamayyarsa Lionel Messi na Barcelona

ratar 17.

Kafin ya ci kwallon Mayoral ne ya fara sa zakarun na Turai a gaba minti takwas da shiga fili, amma kuma minti biyu kafina tafi hutun rabin lokaci sai Aubameyang ya zare daya.

Sannan wasu minti biyun da dawowa fili bayan hutun sai dan wasan na Gabon ya sake daga ragar Real Madrid cikin ruwan sanyi bayan wani dan gumurzu da farko, wasa ya zama 2-2.

Can a minti na 81 ne kuma sai kungiyar ta Spaniya ta tsira da bal ta uku ta hannun Lucas Vazquez.

Wasan ya kasance kamar yadda Real Madrid ta yi wa bakin nata shigar sauri ta daga ragarsu har sau biyu cikin minti hudu, haka su ma, suka yi mata, amma cikin kashi dai-dai na wasan.

Kungiyar ta Zidane daman tuni tana ta biyu a rukunin nasu ne a bayan Tottenham, kuma za a iya hada ta a wasan zagaye na gaba, da Roma ko Besiktas ko Paris St-Germain ko Manchester City ko Manchester United ko kuma Liverpool a hadin da za a yi ranar Litinin.