Za a yi gwajin na'urar bidiyon taimaka wa lafiri a wasan FA na Crystal Palace da Brighton

Karawar Crystal Palace da Brighton a watan Nuwamba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Crystal Palace da Brighton sun yi canjaras ba ci a wasansu na Premier ranar 27 ga watan Nuwamba

A karon farko a Ingila za a yi gwajin amfani da fasahar taimaka wa alkalin wasa ta hoton bidiyo, a wata gasa, a karawar da za a yi tsakanin Brighton da Crystal Palace ta wasan cin kofin FA zagaye na uku.

Daman tun a watan Maris hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce za a yi gwajin a gasar cin kofinta na FA, kuma an so a fara gwajin ne a wasan da Tottenham za ta yi a gida da AFC Wimbledon.

Ana amfani da fasahar ne wurin warware takadda uku a wasan, tantance shigar kwalllo raga, da fanareti da kuma laifin bayar da jan kati na kora, sanna kuma alkalin wasa zai iya amfani da ita idan ya gamu da matsalar tantance ainahin dan wasan da ya aikata wani abu.

A Birtaniya an fara amfani da na'urar a wasan da aka yi na sada zumunta tsakanin Ingila da Jamus a watan Nuwamba, ko da yake ba a kai ga wata bukata ko takaddama da alkalin wasa zai yi amfani da ita ba.

Ana amfani da fasahar a kasashen duniya daban-daban tun lokacin da majalisar hukumomin kwallon kafa na duniya ta amince da fara gwajinta a 2016.

Tun lokacin da aka yi amfani da ita a gasar cin kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa a watan Disamba na wannan shekara, ake ganinta a gasar kasashe kamar, Bundesliga ta Jamus da Serie A ta Italiya da kuma Major League Soccer ta Amurka.