Wa zai ci gasar Ballon D'Or a yau Ronaldo ko Messi?

Neymar da Mbappe da Kevin de Bruyne da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Cristiano Ronaldo da Messi su suka ci kyautar tara ta karshe a tsakaninsu

Dan wasan Portugal da Real Madrid Cristiano Ronaldo, wanda ke rike da kambin gwarzon dan kwallon duniya a yanzu da takwaransa na Argentina da Barcelona Lionel Messi su ne 'yan wasa biyu da ake ganin cikinsu daya zai sake karbar kambin na Ballon D'Or na shekara shekara a daren nan a birnin Paris.

'Yan wasan biyu su suka samu kambin tara da aka bayar a baya a tsakaninsu, kuma ana ganin a wannan karon dan wasan na Real Madrid zai karbe kambin ya zama yana da biyar daidai da na abokin hamayyara tasa Messi.

Dan Senegal da kungiyar LIverpool Sadio Mane da kuma takwaransa na Gabon da kungiyar Borussia Dortmund, Pierre Emerick Aubameyang su kadai ne 'yan wasan Afirka biyu daga cikin 30 da ke takarar kambin na bana.

George Weah, na Liberia wanda ya ci kambin a shekarar 1995, shi kadai ne dan Afirka da ya taba karbar kambin na Ballon D'Or tun lokacin da aka kirkiro da kyautar a shekarar 1962.