Kofin Europa: Arsenal ta yi wa Bate zazzaga 6-0

Lokacin da Jack Wilshere ke ci wa Arsenal kwallon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A bana sau hudu ana sako Jack Wilshere a wasan Premier inda yake yin canji

Jack Wilshere ya ci bal dinsa ta farko tun watan Mayu na 2015, bayan da Arsenal ta kammala wasanta na rukuni na 8, (Group H), a gasar Europa da nasara 6-0 a kan Bate Borisov.

Daman tuni Gunners din sun tsallake zuwa mataki na gaba na zagayen kungiyoyi 32, na sili-daya-kwale, tun kafin wasan na karshe.

Mathieu Debuchy ne ya fara ci wa Arsenal kwallo minti 11 da shiga fili, sannan a minti na 37 Walcott ya ci ta biyu, kafin kuma Wilshere ya kawo karshen kamfar zura kwallon da yai fama da ita ta shekara biyu a minti na 43.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne sai Polyakov na bakin ya ci kansu minti shida da shigowa, sannan Giroud kuma ya ci fanaretin da suka samu a minti na 64, wadda bayan ya buga ta farkoya ci alkalin wasa ya sa ya sake kuma bai kuskure ba.

El Neny ne ya zura wa Arsenal bai din karshe ta shida minti goma bayan cin fanaretin, wanda hakan ya tabbatar wa da Arsenal din gama wasannin nata na rukuni da gwajin wasu daga cikin matasan 'yan wasanta.