Kofin Europa: Everton ta kare da cin Apollon 3-0

Ademola Lookman da Fraser Hornby ( na dama) Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ademola Lookman yana wasa a bangaren hagu ne tare da Fraser Hornby (na dama), wanda wannan ne wasansa na farko a Everton

Ademola Lookman ya zura kwallo sau biyu a raga a karawar da Everton ta kawo karshen wasanta na kofin Europa da nasara daya kawai da ta yi a kan Apollon Limassol da ci 3-0.

Saboda wasan hamayya da ke tsakanin kungiyar da Liverpool a ranar Lahadi, Everton din ta ajiye 'yan wasa 11 daga cikin wadanda suka taka mata leda a nasara da ta yi da Huddersfield.

Shi ma sabon kociyan kungiyar Sam Allardayce bai bi su zuwa wasan na Cyprus ba saboda ya je ganin likita.

Lookman ya fara ci wa Everton, wadda tuni ta fice daga gasar ta Europa, kwallon farko a minti na 21, sannan ya kara ta biyu minti bakwai tsakani, kafin kuma Nikola Vlasic ya ci ta uku a minti na 87.

Everton ta ci wasa uku kenan a jere duka a karkashin jagorancin kociya daban-daban, da farko tare da kocin rikon kwarya David Unsworth sai wasa na biyu tare da Allardyce, yanzu kuma da Craig Shakespeare.

Nasarar ta sa suka kauce wa kammala wasanninsu na rukuni ba a na karshe ba, sannan suka kaucewa zama kungiyar Ingila ta farko da ba ta ci wasa ko daya ba na rukuni a gasar Europa.

Atalanta ce ta zama ta daya a rukunin na biyar (Group E), sakamakon doke Lyon 1-0, wadda ta sa dan wasanta na gaba Willem Geubbels mai shekara 16 da wata hudu ya yi wasan minti 45.

Sanya shi a wasan ya sa ya zama mafi kankanta da ya buga wasan kofin Turai a shekara goma. da ta yi 1-0.