Philippe Coutinho na son barin Liverpool

Philippe Coutinho Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun bayan da ya dawo daga jinya Philippe Coutinho ya ci kwallo tara a wasa 13 da ya yi wa Liverpool

Dan wasan Liverpool na Brazil, Philippe Coutinho ya tabbatar cewa ya so tafiya Barcelona a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, kuma a yanzu ma ba shi da tabbas kan zamansa a Liverpool.

Dan wasan mai shekara 25, ya gamu da cikas a wurin kungiyarsa bayan da ta ki amincewa da bukatarsa ta tafiya a watan Agusta.

Sannan ta yi watsi da tayi har uku da Barcelona ta yi a kan Coutinhon da cewa ba na sayarwa ba ne, bayan daman ya kulla yarjejeniyar shekara biyar a farkon shekaran nan ta 2017.

Barcelona ta taya shi da farko fam miliyan 72, ta kara zuwa 90, har kuma ta kai miliyan 114, domin dai ta same shi ya maye gurbin Neymar wanda ta sayar wa PSG miliyan fam miliyan maitan, wato 200

Yanzu dai dan wasan ya ce bai san abin da zai faru ba ko za a sake zawarcinsa a lokacin kasuwar watan Janairu na shekara mai kamawa?