Jordan Henderson: Keftin din Liverpool 'na da aikin da ya fi wahala a tamaula' - Jurgen Klopp

Jordan Henderson Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jordan Henderson bai buga wasan da suka yi da Spartak Moscow ba, duk da cewa Red ba su sami zuwa mataki na gaba ba a wanna lokacin

Jordan Henderson yana da aikin da ya fi ko wane wahala a tamaula wajen maye gurbin Steven Gerrard a matsayin keftin din Liverpool in ji koci Jurgen Klopp.

Wasu magoya bayan sun soki dan wasan tsakiyar Ingila, wanda ya zauna a kan benci a nasarar 7-0 da the Reds suka samu kan Spartak Moscow ranar Laraba.

"Ina zama a wannan birnin kuma ina jin kadan da yadda mutane suke magana game da birnin ," in ji Klopp.

"Wani dan wasa mai muhimmanci ne gare mu - ban san me ya sa dole in bayyana hakan ba."

Henderson ya maye gurbin Gerrard, wanda ya ci kwallo 186 a wasanni 710 da ya buga wa Liverpool, a matsayin keftin a lokacin bazarar shekarar 2015 a lokacin da gwarzon Reds din na ya koma LA Galaxy.

"Kasancewa keftin din Liverpool shi ne abin da ya fi wahala a duniya domin mutumin da ya rike wannan mukamin a da shi ne Steven Gerrard. Abin tausayi ne, ya gama wasan kwallon kafa , ba za mu iya samu mu dawo da shi ba," in ji Klopp - wanda aka ba shi aikin koci bayan Gerrard ya tafi.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba