Wanene zai lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar BBC na bana?

Wanene zai lashe gasar gwarzon dan kwallon kafar BBC na bana?

Victor Moses (Nigeria), Sadio Mane daga Senegal, Mohamed Salah (Masar), Pierre-Emerick Aubameyang daga Gabon da kuma Naby Keita dan kasar Guinea su ne ke takarar lashe gasar dan kwallon Afirka na BBC na bana. Mun tambayi wasu 'yan Afirka kan wanda suke so ya lashe gasar. Idan anjima ne da misalin karfe 6:30 na yamma a agogon Najeriya da Nijar za a sanar da wanda ya lashe ta.