Borrussia Dortmund ta raba gari da kocinta

Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar,
Image caption Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar,

Borrussia Dortmund ta kori kocinta Peter Bosz, bayan da ya shafe wata bakwai yana jan ragamar kungiyar.

Kungiyar ta kuma nada tsohon kocin Cologne, Peter Stoger, a matsayin kocin rikon kwarya har zuwa karshen kakar bana.

A makon da ya gabata ne Cologne ta kori kocinta Stoger.

Kungiyar ta Dortmund ta gaza samun nasara tun watan Satumba, ko a wasanta na ranar Asabar ma Werder Bremen ce ta doketa da ci 2-1 a gida.

Labarai masu alaka