Chelsea za ta hadu da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

UEFA Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea za ta kara da Barcelona a sabon jadawalin da aka fitar na kungiyoyi 16 da za su fafata a Gasar Zakarun Turai.

An fitar da jadawalin ne a hedkwatar hukumar UEFA da ke birnin Nyon na kasar Switzerland ranar Litinin.

  • Juventus da Tottenham
  • FC Basel da Manchester City
  • Porto da Liverpool
  • Sevilla da Manchester United
  • Real Madrid da PSG
  • Shakhtar Donetsk da Roma
  • Bayern Munich da Beskitas.

Za a fara wasaninin a ranakun 13 da 14, sai ranakun 20 da 21 duka ga watan Fabrairun shekarar 2018.

Hakazalika, kungiyoyin za su kara fafata a ranakun 6 da 7, sai kuma 13 da 14 ga watan Maris din badin.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka