Kofin Europa: Arsenal za ta hadu da FK Ostersunds, Celtic da Zenit

Theo Walcott na murnar cin kwallo a karawarsu da Bate Borisov a gasar Europa Hakkin mallakar hoto APf
Image caption Theo Walcott da Welbeck a lokacin wasan da suka casa Bate Borisov a gasar Europa

Arsenal za ta hadu da FK Ostersunds ta Sweden yayin da aka hada Celtic da Zenit St Petersburg ta Rasha a matakin wasan kungiyoyi 32 na gasar kofin Turai na Europa.

Arsenal wadda ta zama ta daya a rukuninta na gasar ta Europa za ta fara ziyartar kungiyar ta Sweden ne a matakin wasan na sili-daya-kwale.

Celtic kuwa ta gama a matsayi na uku ne a rukuninsu na gasar zakarun Turai ta Uefa, saboda haka ta fado kasa zuwa gasar ta Europa, inda dukkanin kungiyoyi 32 da suka kai matakin za su yi fafatawar farko a ranar 15 ga watan Fabrairu na shekara mai kamawa, da karfe shida na yamma agogon Najeriya.

Sannan kuma sai a ranar 22 ga watan na Fabrairu na shekarar ta 2018 da karfe 9.05 na yamma agogon Najeriya, duka kungiyoyi 32 za su yi wasa na biyu, wanda daga nan ne za a tankade rabi wato 16, zuwa mataki na gaba.

Ga yadda jadawalin da aka fitar ranar Litinin din nan a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa, a birnin Nyon na Switzerland na gasar ta kofin Europa yake:

Borussia Dortmund v Atalanta

Nice v Lokomotiv Moscow

FC Copenhagen v Atletico Madrid

Spartak Moscow v Athletic Bilbao

AEK Athens v Dynamo Kiev

Celtic v Zenit St Petersburg

Napoli v RB Leipzig

Red Star Belgrade v CSKA Moscow

Lyon v Villarreal

Real Sociedad v Red Bull Salzburg

Partizan Belgrade v Viktoria Plzen

Steaua Bucharest v Lazio

Ludogorets v AC Milan

Astana v Sporting Lisbon

FK Ostersunds v Arsenal

Marseille v Braga