An jefi Jose Mourinho sannan an fasa wa Mikel Arteta na Man City kai

Pep Guardiola da Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An jefi Mourinho da madara da ruwa a lokacin da yake cacar-baki da golan Manchester City, Ederson a kofar dakin sa kaya na 'yan City

An jefi kociyan Manchester United Jose Mourinho da ruwa da madara shi kuma mai koyar da 'yan wasan Manchester City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka yayin wata sa-in-sa bayan wasan kungiyoyin biyu ranar Lahadi.

'Yan United sun harzuka ne kan abin da suke gani ya wuce-makadi-darawa a lokacin murnar da 'yan wasan City suke yi bayan sun bi abokan hamayyar tasu har gida Old Trafford sun casa su 2-1, suka yi musu fintinkau da maki 11 a teburin Premier.

'Yan wasan City sun rika burede a gaban magoya bayansu bayan an tashi daga wasan, kuma 'yan tawagar horar da 'yan wasan sun nemi kociyansu Pep Guardiola shi ma ya bi sahu a cashe da shi amma ya ki.

Bayan 'yan wasan gaba daya sun kama hanyarsu zuwa dakunanunsu na sauya tufafi, a nan ne ake ganin Mourinho ya nuna bacin ransa a kofar dakin tawagar Man City, a kan hanyarsa ta zuwa wajen hira da 'yan jarida.

'Yan Manchester City sun mayar da martani inda mai tsaron ragarsu dan Brazil Ederson da Mourinho suka yi cacar-baki da harshen Portugal.

Daga nan ne kuma aka jefi Mourinhon da wani kwalin madara da aka bari a dakin na bakin, ko da yake ba ta bata shi ba amma ta bata wani daga cikin ma'aikatansa.

Kuma an ga kociyan ya shiga dakin alkalin wasa a lokacin daga bisani ya fito ya tafi wajen hira da 'yan jarida, amma dai bai yi maganar abin da ya faru ba a yayin ganawar.

Hakkin mallakar hoto CAVENDISH PRESS
Image caption Mikel Arteta ya rufe goshinsa lokacin da ya je filin atisaye na Manchester City ranar Litinin da safe

An ga mai horar da 'yan wasan City motsa jiki Mikel Arteta ya ji rauni a ka amma ba a san yadda ya ji ciwon ba, kuma dukkanin bangarorin kungiyoyin biyu sun ce ba a ba wa hammata iska ba.