Mamadou Sakho na Crystal Palace ya tafi jinyar tsawon lokaci

Mamadou Sakho (a dama) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mamadou Sakho (a dama) ya yi wa Faransa wasa sau 28

Dan wasan baya na kungiyar Crystal Palace a Premier, Mamadou Sakho ya ji raunin da zai yi jinya ta tsawon lokaci a sharabarsa.

Sakho ya ji raunin ne a wasan da suka yi canjaras 2-2 ranar Asabar da Bournemouth, kociyan Palace Roy Hodgson yana ganin dan wasan zau dauki makwanni kafin ya warke.

Kungiyar za ta kuma duba yanayin Yohan Cabaye, wanda aka sauya shi a wasan da suka yi da Bournemouth, saboda dan rauni da ya ji.

Ita kuwa kungiyar Watford ta daukaka kara a kan jan katin da aka ba wa Marvin Zeegelaar a lokacin wasansu da Burnley a karshen mako.

Sannan Kiko Femenia ya samu 'yar matsalar cirar nama a cinyarsa, wadda kungiyar ke dubawa, yayin da shi kuwa Miguel Britos ke dab da warwarewa ya dawo taka wa kungiyar leda nan ba da jimawa ba.