Harry Kane ya kusa kai Alan Shearer yawan kwallaye

Harry Kane heads in his first goal for Tottenham against Stoke on Saturday Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Harry Kane ya ci kwallaon shi na farko a karawar Tottenham da Stoke ranar Lahadi

Ya fi Cristiano Ronaldo da Neymar da kuma West Brom da Crystal Palace - yawan kwallaye a shekarar 2017.

Iya zura kwallo a raga na dan wasan gaban Tottenham din ya ci gaba ranar Asabar inda ya ci kwallo biyu a wasan da Spurs ta lallasa Stoke da 5-1 a filin wasa na Wembley.

Kane ya ci kwallo 33 cikin wasannin gasar Firimiya 32, wadanda suke cikin kwallaye 50 da ya ci cikin wasanni 48 a dukkan gasa da ya buga wa kulob dinsa da kasarsa.

Dan shekara 24 din ya yi kusa da tarihin da mutumin da ake ganin Kane zai gada ya kafa- tsohon dan wasan gaban Blackburn da Newcastle da kuma Ingila, Alan Shearer.

Wadanda suka fi cin kwallaye a gasar Firimiya a shekara cikin tarihi

Dan wasa Kulob Kwallaye Shekara
Alan Shearer Blackburn 36 1995
Robin van Persie Arsenal 35 2011
Thierry Henry Arsenal 34 2004
Harry Kane Tottenham 33 2017
Alan Shearer Blackburn 30 1994
Les Ferdinand Newcastle 30 1995
Ruud van Nistlerooy Manchester United 30 2003

Kwallayen Kane 33 suna daidai da ko kuma sun fi na kungiyoyin kwallon kafar gasar Firimiya a wannan shekarar - na Swansea da Burnley (jumulla sun da 33), Crystal Palace (tana da 31) kuma West Brom (tana da 30).

Kwallaye biyun da Kane ya ci Stoke sun sa jumullar kwallayen da ya ci a gasar Firimiya sun kai 90, matakin da ya cimma cikin wasanni 131.

Shearer kadai ne kawai fi saurin kai wannan matakin a tarihin gasar Frimiya , inda ya kai matakin cikin wasanni 113 kafin ya kai ga kafa tarihin cin kwallaye 260 a wasanni 441 .

Shearer ya cigaba da taka leda har ya kai shekara 35. Idan Kane ya cigaba da murza leda har ya kai wadannan shekaraun, zai samu damar shekara 11 inda zai nemi cin kwallaye 170 da yake bukata domin kamo iya kwallayen Shearer, abin da zai kai ga in yana cin kwallaye 15 a ko wace kaka har zuwa karshen kakar 2028-29 .

Kane da Shearer - tarihin cin kwallo a kakarsu takwas ta farko
Kane Shearer
kaka Kulob Wasanni Kwallaye Kaka Kulob Wasanni Kwallaye
2010-11 Leyton Orient (loan) 18 5 1987-88 Southampton 5 3
2011-12 Millwall (loan) 22 7 1988-89 Southampton 10 0
2012-13 Leicester, Norwich (both loan), Tottenham 19 2 1989-90 Southampton 26 3
2013-14 Tottenham 10 3 1990-91 Southampton 36 4
2014-15 Tottenham 34 21 1991-92 Southampton 41 13
2015-16 Tottenham 38 25 1992-93 Blackburn 21 16
2016-17 Tottenham 30 29 1993-94 Blackburn 40 31
2017-18 (kawo yanzu) Tottenham 15 12 1994-95 Blackburn 42 34

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba