Man City ba ta wuce makadi da rawa ba a murnar doke Man Utd - Pep Guardiola

Guardiola da Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tawagar Guardiola, Manchester City ta bayar da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester United bayan ta doke ta a ranar Lahadi

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya musanta cewa 'yan wasansa sun wuce makadi da rawa a yayin murnar cin abokan hamayyarasu Manchester United da suka yi ranar Lahadi, 2-1.

Kociyan dan kasar Spaniya ya ma kara da cewa shi da kansa ne ya karfafa wa 'yan wasan nasa da su yi bureden.

A yayin murnar ne shi kuma kociyan United Jose Mourinho aka watsa masa ruwa da madara a kofar dakin sauya tufafi na Man City a filin na Old Trafford, lokacin da yake musayar kalamai da mai tsaron ragar City, dan Brazil, Ederson.

Haka kuma a wannan lokacin ne aka fasa wa mai horar da 'yan wasan City kan motsa jiki Mikel Arteta, kai da robar ruwa, amma ba a san waye ya jefe shi ba, sannan dukkanin bangarorin kungiyoyin biyu sun ce ba a ba wa hammata iska ba a lokacin.

Guardiola ya ce ko alama abin da tawagar tasa ta yi daidai ne da wanda ta yi lokacin da suka doke Southampton.

A ranar Litinin hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ba wa kungiyoyin biyu wa'adin har zuwa ranar Laraba da su bayar da ba'asi kan abin da suka san ya faru a lokacin.

Guardiola ya ce ba ya fatan abin da ya faru a can kofar dakin sauya tufafin na kungiyoyin lokacin ya sake faruwa.

Ya kara da cewa ya kamata mutane su fahimci cewa suna fa murna ne a lokacin. Kuma duk wata kungiya a duniya idan ta yi nasara a wasan hamayya tana matukar murna da farin ciki.

Ya ce lokacin da suka doke Bayern sun yi murna, haka ma da Barcelona sun yi burede.