An ji wa Oscar Pistorius rauni a gidan yari

Oscar Pistorius tare da jami'an tsaro Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu Oscar Pistorius (na hagu a 2016) da laifin kashe budurwarsa a shekarar 2015

An raunata tsohon dan tseren Afrika ta Kudu Oscar Pistorius a wani fada da suka yi a gidan yarin da yake, kasa da mako biyu da lillinka hukuncinsa na kisan budurwarsa Reeva Steenkamp.

Wani kakakin hukumar gidan yarin ya sheda wa BBC cewa an ji wa dan tseren gasar Olympic ta nakasassun ne raunin a yayin sa-in-sa kan amfani da wayar tarho ta gidan kason.

Kakakin ya ce Pistorius wanda aka daure shekara 13 da wata biyar ya dan kurje ne a lokacin rigimar, amma ba wani ciwo mai tsanani da ya ji.

Mai magana da yawun hukumar gidan yarin a Attridgeville Correctional Centre, Singabakho Nxumalo, ya ce Pistorious ya yi rigima da wani dan gidan kason ne a kan amfani da wayar tarhon ne.

Rigimar ta faru ne a ranar shida ga watan nan na Disamba, kwana 10 bayan da masu gabatar da kara na kasar ta Afirka ta Kudu suka yi nasarar gamsar da kotu cewa akwai bukatar kara wa'adin shekara shida da aka yanke wa tsohon dan tseren na Olympic.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pistorius ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp a ranar masoya ta shekarar 2013

A watan Nuwamba kotun kolin kasar ta daukaka kara ta yanke wa Pistorious hukuncin zaman gidan maza na shekara 15, mafi karancin da dokar Afrika ta Kudu ta tanada a kan laifin kisan kai, wanad tuni ya yi rabin wa'adin.

A da dai kotu ta samu Pistorious da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp ba da niyya ba, a ranar masoya ta 2013 amma kuma daga baya kotun kolin ta daukaka kara ta sauya hukuncin inda ta same shi da laifin kisan da gangan.