Marvin Zeegelaar: An yi watsi da bukatar janye jan katin dan wasan na Watford

Lokacin da Marvin Zeegelaar ya yi ketar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Marvin Zeegelaar ya koma Watford ne daga Sporting Lisbon a kan fam miliyan 2.75

An yi watsi da bukatar janye jan katin da aka ba wa dan wasan baya na Watford Marvin Zeegelaar a karawarsu da Burnley ta ranar Asabar.

Alkalin wasa ya kori dan wasan mai shekara 27 saboda keta kafa bibbiyu da lafirin yake ganin ya yi wa Steven Defour a wasan da Watford ta yi nasara 1-0 a gidan Burnley, Turf Moor.

Dan wasan na Holland yanzu ba zai buga wasan da za su yi na lokacin Kirsimeti da sabuwar shekara ba, inda za su kara da Crystal Palace da Huddersfield da kuma Brighton.

An jiyo kociyan Watford Marco Silva a ranar Asabar yana cewa hukuncin da aka yi wa dan wasan ya yi tsanani.

Bayan wasan Silva ya kara da cewa, ba laifi ne na bayar da jan kati ba, katin ya sauya komai a wasan, domin bayan minti biyu ko uku da bayar da shi suka ci, in ji kociyan yana korafi.

Watford za ta yi fatan ganin ta yi nasara a wasanta na farko a cikin hudu, idan suka hadu da tawagar Roy Hodgson, Crystal Palace a ranar Talatar nan.