Fifa ta hukunta Najeriya saboda sa dan wasan da bai cancanta ba

Alkalin wasa lokacin da ya ba wa Abdullahi Shehu katin gargadi a wasan Najeriya da Zambia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An ba wa Abdullahi Shehu na Najeriya katin gargadi na biyu a wasan neman tikitin gasar kofin duniya ta 2018 a karawarsu da Zambia

An hukunta hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) saboda sanya dan wasan da bai cancanta ba a karawar kasar da Algeria ranar 10 ga watan Nuwamba na 2017.

A hukuncin an ayyana Najeriya ta saryar da wasan tare da ba wa Algeria nasara da ci 3-0, da kuma cin tarar hukumar kwallon ta Najeriya sama da naira miliyan biyu.

Hukunci ya danganci dan wasan kasar ne Abdullahi Shehu, wanda Najeriya ta sa a haduwarta da Algeria duk da cewa ya kamata ya tsallake wasa daya sakamakon katin gargadi da aka ba shi a wasa biyu daban-daban na gasa daya.

Sai dai kuma hukuncin ba shi da wani tasiri ga sakamakon karshe na gasar ta neman gurbin gasar cin kofin duniya, saboda daman Najeriya tuni ta cancanci zuwa gasar kafin wasan, kuma ita Algeriya, an rigaya an fitar da ita.