Tottenham:Toby Alderweireld ya tafi jinya sai Fabrairu

Toby Alderweireld lokacin da ya ji rauni Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Toby Alderweireld ya rasa wasa takwas tun lokacin ya ji raunin a karawarsu da Real Madrid

Dan wasan baya na Tottenham Toby Alderweireld ba zai sake taka leda ba daga yanzu har zuwa watan Fabrairu na shekara mai kamawa saboda raunin da ya ji a cinyarsa kamar yadda kociyansu Mauricio Pochettino ya tabbatar.

Dan bayan na Belgium mai shekara 28, bai yi wasa ba tun lokacin da ya samu matsalar a karawar da suka ci Real Madrid 3-1 ta gasar zakarun Turai ranar 1 ga watan Nuwamba.

A tsawon wannan lokacin Tottenham din ta yi nasara sau biyu ne kawai a wasa shida da ta yi na gasar Premier.

An ruwaito kociyansu Pochettino yana cewa ba abin da za su iya yi da kaddara, abin da ya faru ya riga ya faru, dan wasan ya ji rauni kuma ba zai sake wasa ba sai a watan Fabrairu.

Kungiyar ta Spurs tana wasa 10 a gasa daban-daban tsakanin yanzu da watan na Fabrairu, wasannin da suka hada da na Premier, da za ta yi da Manchester City da kuma Manchester United.

Sannan kuma za ta yi wasan hamayya na arewacin Landan, wato karawarta da Arsenal ta gaba ranar 10 ga watan na Fabrairu a Wembley.

Sannan kuma bayan kwana uku za ta yi wasanta na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai da Juventus.

A ranar Laraba ne Tottenham din da ke matsayi na shida a teburin Premier za ta fafata da ta 13, Brighton.