Real Madrid na harin Kofin Duniya na uku

'Yan wasan Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid na fatan kammala wannan shekara da kofinta na biyar a birnin Abu Dhabi a wannan makon

Zakarun Turai Real Madrid za su fara kokarin daukar kofin duniya na kungiyoyi a karo na uku, inda za su yi wasan kusa da karshe da kungiyar Al Jazira a birnin Abu Dhabi a ranar Laraba.

Kungiyar ta Zinedine Zidane na harin zama ta farko a tsakanin sauran takwarorinta zakaru da za ta ci kofin haka a jere.

Abokiyar hamayyarta ta Spaniya, Barcelona ita ce kadai ta ci kofin na duniya na kungiyoyi sau uku, tun lokacin da aka bullo da gasar a shekara 2000.

Gasar tana kunsar zakarun nahiyoyi ne shida na Fifa, tare da kungiyar da ta dauki kofin lig na kasar da za a gudanar da ita.

An daga wa Real Madrid kafa a gasar zuwa matakin wasan na kusa da karshe, kuma kungiyar da za su yi da ita, Al Jazira, ta samu tikitin gasar ne saboda ita ce ta dauki kofin zakarun gasar kasashen yankin tekun Persia.

Kungiyar ta kai wannan mataki ne na karawa da Madrid bayan da ta doke takwararta ta Auckland City ta New Zealand a wasan raba-gardama.

Bayan wannan kuma ta yi galaba a kan Urawa Red Diamonds ta Japan a wasan dab da na kusa da karshe na gasar.

Real Madrid ta dauki kofin a shekara ta 2014 da 2016, kuma wannan shi ne zai kasance kofi na biyar da zakarun za su dauka a wannan shekara mai karewa ta 2017.

A daya wasan na kusa da karshe kungiyar Gremio ta kasar Brazil za ta hadu da Pachuca daga Mexico.