Wales za ta ladabtar da shugaban hukumar kwallon kafarta

Jonathan Ford Hakkin mallakar hoto OTHERS
Image caption Maganar da Jonathan Ford ya yi cewa ba za su dauki dan Ingila kociya ba, ita ce ta jefa shi cikin matsala

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta fara shirin daukar matakin ladabtar da shugabanta Jonathan Ford saboda ya ce kociyan tawagar yankin na gaba zai iya kasance dan kasar waje amma dai ba dan Ingila ba.

Hukumar ta kafa kwamitin mutane uku da zai yi bincike a kan wata hira da BBC ta yi da shugaban, wadda a ciki ya yi wannan kalami, har ma yake cewa a ko da yaushe kusan suna bayar da fifiko a kan 'yan Wales saboda su suna nuna sha'awa a kan aikin.

A yayin taron majalisar zartarwa ta hukumar kwallon kafar ta Wales ne aka taso da maganar hirar ta BBC da Ford, inda aka neme shi da ya fita daga dakin taron.

Kwamitin ladabtarwar zai gana domin ya titsiye Ford a kan lamarin, ko da yake zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba yayin da Wales din ke kokarin maye gurgin Chris Coleman, wanda ya bar aiki saboda kasa sama wa tawagar yankin gurbin gasar kofin duniya ta 2018, da za a yi a Rasha.

Mataimakin Coleman Osian Roberts da tsohon dan wasan Wales na gaba Craig Bellamy da John Hartson da kuma Ryan Giggs dukkaninsu sun nuna sha'awarsu ta samun aikin kociyan.

Kuma tun da dadewa hukumar kwallon ta Wales tana sha'awar ba wa tsohon dan wasansu na gaba da kuma Manchester United.

Sannan shi ma Tony Pulis, dan Wales din wanda a watan da ya wuce aka kore shi daga aikin kociyan West Bromwich Albion na daga cikin wadanda ake duba yuwuwar ba su aikin na horar da tawagar kwallon ta Wales.