Ba na nadamar bata wa Mourinho rai - Guardiola

Pep Guardiola da Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guardiola ya ce indai ran Mourinho ne ya baci kan murnarsu ta cin Man United to shi ba ya nadama

Pep Guardiola ya ba wa Manchester United hakuri da cewa idan har yadda suka cashe lokacin da suka doke abokan hamayyar tasu 'yan United din ba su ji dadi ba, amma kuma ya ce ba ya nadama idan ran Mourinho ne ya baci a kan lamarin.

Kociyan dan kasar Spaniya ya ce, indai har yadda suka yi wannan murna da farin ciki ta cin Manchester United 2-1 a Old Trafford sun bata wa kungiyar rai, amma ba wani dan wasa daya ba ko Jose Mourinho, to yana bayar da hakuri a kai.

Sai dai Guardiolan ya jaddada dama da 'yancin 'yan wasansa na nuna farin cikinsu a kan nasarar da ta sa suka ba wa abokan hamayyar tasu tazarar maki 11 a teburin Premier.

Ya ce dole ne su yi farin ciki a wannan lokaci, amma idan mutane sun kasa fahimtar hakan to sai dai ya ce wannan su ta shafa, domin wasa ne na hamayya suka yi nasara, nasara kuma ta 14 a jere.

A lokacin bureden da kuma sa-in-sar da aka samu bayan da Mourinho ya nuna damuwa kan abin da ya dauka zakewar 'yan City din a murnar, an watsa wa kociyan na United madara da ruwa ko da yake ba su bata shi ba, amma sun samu wani jami'inshi.

Mourinho ya yi gugar zana kan abin da ya faru a lokacin da cewa matsala ce ta bambancin dabi'a da kuma bambancin ilimi.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ba wa kungiyoyin biyu wa'adin zuwa Larabar nan su ba ta bahasi kan lamarin.