An taya Newcastle fam miliyan 300

Rafael Benitez Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Kociya Rafael Benitez na fatan samun kyakkyawan labarin sayar da kungiyar bayan wasansu da Everton

Mai kungiyar Newcastle Mike Ashley da 'yar kasuwar Birtaniyan nan Amanda Staveley sun gana a karon farko domin tattaunawa a kan yadda za a sayar da kungiyar ta gasar Premier.

BBC ta fahimci cewa mutanen biyu sun gana ne a wani gidan cin abinci na Indiyawa a Landan a makon da ya wuce, bayan da kamfanin da matar take tafiyarwa - PCP Capital Partners, ya yi sabon tayi na kusan fam miliyan 300 a kan kungiyar.

Ya zuwa lokacin hada wannan labari kungiyar ta Newcastle ba ta ce komai ba a kai, amma kuma ba ta musanta ganawar mutanen ba.

A watan Oktoba Ashley ya ce yana son sayar da kungiyar bayan da ya mallake ta tsawon shekara goma.

Dan kasuwar da ya tafi Amurka amma yanzu ya dawo Ingila yayin da ake ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.

In dai har cinikin ya kaya to sai dole ya samu amincewar hukumar gasar Premier, wanda kuma zai dauki kwana talatin.

'Yar kasuwa Staveley, ita ce ta shiga tsakani wajen cinikin sayar wa Sheikh Mansour Manchester City a 2009, kuma rahotanni sun ce ita ce ta jagoranci tayin fam miliyan 400 da kamfanin Dubai International Capital ya yi a kan Liverpool a 2008.

Shi dai Ashley, mai shekara 53 ya jawo rabuwar kai a kungiyar Newcastle, inda wasu magoya baya a kai a kai suke nuna rashin amincewarsu da yadda dan kasuwar yake tafiyar da kungiyar.

Attajirin ya sayi Newcastle ne a kan fam miliyan 134.4 a shekara ta 2007.

Sau biyu kungiyar na faduwa daga Premier a tsawon shekara goma da ta yi a hannun attajirin, kuma yanzu tana matsayi na 16 a gasar bayan wasa 16, bayan haurowa da ta sake yi gasar a karkashin kociya Rafael Benitez.