Boksin: An wanke Tyson Fury ya dawo dambe

Tyson Fury Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rabon da Tyson Fury ya yi dambe tun lokacin da ya yi nasara a kan Wladimir Klitschko a watan Nuwamba na 2015

Hukumar kula da harkokin damben boksin ta Birtaniya za ta waiwayi batun dakatar da lasisin damben Tyson Fury dan kasar ta Birtaniya a watan Janairu.

Hukumar hana amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni ta Birtaniya ce ta haramta wa Tyson mai shekara 29 dambe saboda samunsa da laifin amfani da wata kwayar da ta hana amfani da ita a shekara ta 2015.

An matsar da wa'adin hukuncin baya, wanda hakan ke nufin tsohon dan damben na ajin babban nauyi yana da damar sake yin damben.

Ita kuwa hukumar kula da harkokin damben boksin ta Birtaniya ta soke lasisinsa ne a watan Oktoba saboda matsalar rashin lafiya da ta shafi damuwa.

Haka shi ma dan uwan Tyson Fury din, Hughie Fury, an wanke shi ya sake komawa fagen damben, bayan da aka same shi da laifin amfani da abubuwan kara kuzari a wasa a watan Fabrairu na 2015.

Ba a tuhumi dukkaninsu ba har sai a watan Yuni na 2016, kuma dukkaninsu sun kafe cewa ba da saninsu ko kuma da niyya suka yi amfani da abubuwan kara kuzarin ba.

Shi dai Tyson Fury ya dora alhakin samunsa da alamar amfani da abin kara kuzarin ne a kan cin naman aladen dawa wanda ba a fidiye ba.

A wata sanarwa da shi da dan uwan nasa suka fitar sun ce suna farin ciki an sasanta batun, kuma yanzu za su ci gaba da shiga dambe ba tare da ana kallonsu a matsayin masu zamba ta amfani da abubuwan kara kuzari ba.

A wani wake da ya yi mai cike da habaici Tyson Fury ya caccaki mai hada dambe da zakaran damben masu nauyi na duniya, Anthony Joshua, wato Eddie Hearn, bayan an wanke shi ya dawo fage.

Fury ya kuma caccaki hukumar kula da harkokin damben boksin ta Birtaniya, wadda ta soke lasisinsa a watan Oktoba na 2016 saboda larurarsa ta damuwa, a waken nasa.

Tuni dan damben mai shekara 29 ya kalubalanci mai rike da kambin duniya na hukumar IBF da WBA Anthony Joshua da su dambata a shekara mai kamawa, 2018.

An soke damben da suka yi a watan Fabrairu na 2015, ciki har da wanda Tyson Fury ya doke Christian Hammer, amma an bar sakamakon duk boksin din da suka yi bayan wannan lokacin, har da wanda Tyson din ya doke Wladimir Klitschko.