Kofin Duniya: Real Madrid ta doke Al Jazira 2-1

Cristiano Ronaldo a lokacin da yake rama wa Real Madrid Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristiano Ronaldo ne ya farke kwallon da aka fara cin Real Madrid

Zakarun Duniya Real Madrid za su yi wasan karshe da kungiyar Gremio ta Brazil a gasar kofin duniya na kungiyoyi bayan da ta doke Al Jazira 2-1 a ranar Larabar nan.

A ranar Lahadi ne Real Madrid za ta kara da kungiyar ta Brazil wadda ita ma a Larabar ta fitar da Pachuca ta Mexico a daya wasan na kusa da karshe.

Real Madrid aka fara ci a wasan da ake yi a Abu Dhabi, bayan da dan wasan kungiyar ta Hadaddiyar Daular Larabawa, da Silva ya ci daga musu raga a minti na 41.

Cristiano Ronaldo ne ya rama cin bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 53, kafin kuma Gareth Bale ya kara ta biyu a minti na 81.

Real Madrid za ta kafa tarihin daukar kofin na duniya a jere, wanda zai zamar mata na uku, kuma kofi na biyar da ta dauka kafin a wannan shekara mai karewa ta 2017.

Zakarun na duniya sun dauki kofin a shekara ta 2014 da kuma 2016.

Abokiyar hamayyarta ta La Liga Barcelona ita ce ta taba cin kofin na duniya sau uku tun lokacin da aka kirkiro da gasar a shekara ta 2000.