Arsenal da Liverpool sun yi kasa, Tottenham da Everton sun yi sama

Wayne Rooney ya ci Newcastle Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayne Rooney ya ci kwallo ta tara ke nan a kakar nan

A sauran wasannin da aka yi guda shida na Premier, Wayne Rooney ya ci wa Everton bal din da ta ba ta nasarar farko a Premier, a waje tun watan Janairu a karawar da ta doke Swansea 1-0.

Yanzu Everton tana daidai da ta tara a tebur Watford da maki 22, Newcastle kuma ta zama ta 16 da maki 15.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Lokacin da Arsenal ta kasa zura kwallo a Premier tun wasanta da Chelsea ranar 17 ga watan Satumba

Leicester kuwa ta lika wa Southampton mai masaukinta 4-1, nasarar da ta sa yanzu ta zama ta takwas da maki 26, yayin sa Southampton take ta 11 da maki 18.

Liverpool ta ci gaba da zama a wajen hudun farko bayan da a gidanta ta kasa cin West Brom, suka ta shi canjaras 0-0, lamarin da ya sa Liverpool din take ta biyar da maki 31, ita kuwa West Brom ta zama ta 17 da maki 14.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Roberto Firmino da sauran 'yan wasan gaba na Liverpool sun kasa ratsa bayan West Brom

Kociyan Mancester United Jose Mourinho ya ce zai tafi hutu a Brazil ko birnin Los Angeles na Amurka, idan har ya ga ba su da sauran dama ta fafutukar daukar kofin Premier a bana, bayan da kungiyarsa ta ci Bournemouth 1-0, wadda Lukaku ya lika ta.

United ta ci gaba da bin City a matsayi na biyu da tsiran maki 11, ita kuwa Bournemouth tana mataki na 14 da maki 16.

Tottenham kuwa ta sake komawa cikin hudun farko sakamakon kwallo biyu da Serge Aurier da Son Heun-min suka ci mata, a karawarsu da Brighton.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tottenham ta kankane wasan, ko da yake ta fuskanci matsala daga bakin kafin Aurier ya daga raga

Yanu ta dare matsayi na hudu da maki 31, yayin da Brighton ke matsayi na 13 da maki 17.

Sai kuma Arsenal wadda wasa uku kenan ta yi na Premier ba tare da ta ci ko daya ba, lamarin da ya sa ta koma kasa ta bakwai da maki 30, bayan da ta kasa daga ragar ta 19 a tebur West ham wadda ke gida mai maki 14.