Wales ta fasa ladabtar da shugaban hukumar kwallonta da ya yi bambarma

Jonathan Ford Hakkin mallakar hoto OTHERS
Image caption Jonathan Ford ya bayar da hakuri ne kan bambarmar da ya yi cewa ba za su dauki dan Ingila kociya ba

Hukumar kwallon kafa ta Wales ta fasa daukar matakin ladabtarwa a kan shugabanta Jonathan Ford a game da furucin da ya yi a kwanakin nan cewa kocin tawagar yankin na gaba zai iya kasancewa dan kasar waje amma dai ba dan Ingila ba.

Hukumar ta kafa kwamitin mutane uku ne da zai yi bincike a kan wata hira da BBC ta yi da shugaban, wadda a ciki ya yi wannan kalami, har ma yake cewa a ko da yaushe kusan suna bayar da fifiko a kan 'yan Wales saboda su suna nuna sha'awa a kan aikin.

A yanzu dai an kawo karshen wannan magana, bayan da Jonathan Ford din ya bayar da hakuri kan maganar da ya yi wadda ake gani wata bambarma ce.

A da an shirya kwamitin ladabtarwar zai gana domin ya titsiye Ford a kan maganar, ko da yake zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba yayin da Wales din ke kokarin maye gurbin Chris Coleman, wanda ya bar aiki saboda kasa sama wa tawagar yankin gurbin gasar kofin duniya ta 2018, da za a yi a Rasha.

Mataimakin Coleman Osian Roberts da tsohon dan wasan Wales na gaba Craig Bellamy da John Hartson da kuma Ryan Giggs dukkaninsu sun nuna sha'awarsu ta samun aikin kociyan.

Kuma tun da dadewa hukumar kwallon ta Wales tana sha'awar ba wa tsohon dan wasansu na gaba da kuma Manchester United.

Sannan shi ma Tony Pulis, dan Wales din wanda a watan da ya wuce aka kore shi daga aikin kociyan West Bromwich Albion na daga cikin wadanda ake duba yuwuwar ba su aikin na horar da tawagar kwallon ta Wales.