Kofin Cecafa: Kenya ta kai wasan karshe bayan doke Burundi 1-0

'Yan wasan Kenya Hakkin mallakar hoto OTHERS
Image caption Kenya ta tsira ne bayan da a cikin lokacin fitar da gwani dan wasanta Whyvonne Isuza ya ci mata kwallon

Kenya ta kai wasan karshe na gasar cin kofin majalisar hukumomin kwallon kafa ta Afirka ta tsakiya da ta gabashin Afirka Cecafa, bayan da ta doke Burundi da ci 1-0 a ranar Alhamis.

Bayan kammala minti 90 na wasan ne ba ci aka shiga lokacin fitar da gwani, har mai masaukin baki Kenya, karkashin jagorancin sabon kociyanta Paul Put, wanda a watan da ya wuce ne ya kama aiki ta samu damar jefa kwallon daya.

Dan wasan Kenya Whyvonne Isuza, shi ne ya jefa kwallon bayan minti hudu da fara wa'adin raba gardamar tsakanin 'yan wasan kasashen biyu.

Yanzu tawagar ta Harambee Stars tana jiran wadda za ta yi nasara a daya wasan kusa da karshen a ranar Juma'a tsakanin mai rike da kofi Uganda da kuma Zanzibar.