Klitschko ya sayar da rigarsa naira miliyan 78

Wladimir Klitschko Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wladimir Klitschko ya sha kashi a karo na biyar a tarihinsa na damben a karonsa da Anthony Joshua a Wembley

A watan Afrilu, Wladimir Klitschko ya sayar da rigar da ya shiga fage da ita wadda ke dauke da 'yar ma'adanar bayanan kwamfuta ta tafi da gidanka (USB stick), mai kunshe da hasashen yadda dambensa zai kasance da Anthony Joshua, wanda ya doke shi, a kan fam dubu 160.

Klitschko tsohon zakaran damben boksin na mafiya nauyi na duniya mai shekara 41, ya sanya doguwar rigar ne ya zo dandalin, kafin damben nasa na karshe a Wembley, da zakaran na duniya na yanzu Anthony Joshua.

An dinke 'yar na'urar ne a jikin rigar wadda ke dauke da hasashensa na yadda yake ganin damben zai kaya, wanda ya ce mutumin kawai da zai ji wannan hasashe shi ne wanda ya sayi rigar.

A turmi na goma sha daya Joshua ya doke Klitschko dan Ukraine, wanda tuni ya yi ritaya daga damben boksin din.

Kudin da aka samu na sayar da rigar a wurin wani taron samar da tallafi a Landan ranar Laraba, za a yi amfani da shi ne a ayyukan da Gidauniyar Klitschko ke taimaka wa.