Kaka ya yi ritaya daga tamaula

Kaka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ya zura kwallaye 29 a raga a wasannni 92 da ya buga wa kasarsa Brazil

Tsohon dan wasan kungiyoyin AC Milan da Real Madrid, Kaka, ya yi ritaya daga taka leda.

Dan kwallon mai shekara 35 ya fara taka leda a Sao Paulo.

Yana daya daga cikin 'yan wasa takwas da suka lashe Kofin Zakarun Turai da Kofin Duniya da kuma kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or.

Kaka wanda mabiyin addinin Kirista ne ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi cewa: "Ina godiya ga Ubangiji kan matakin da na kai wanda ban taba tsammani ba. Na gode! Kuma a shirye nake na fara zango na gaba."

Dan wasan ya yi fice ne a iya yanka da zura kwallo a raga kuma ya zura kwallaye 29 a raga a wasannni 92 da ya buga wa kasarsa Brazil.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka