Pep Guardiola: Man City za ta tattauna da kocinta kan kwantiraginsa

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester City za ta tattauna da kocinta Pep Guardiola a lokacin bazara yayin da kungiyar take neman ta zama gagara-badau irin yadda Manchester United ta zama a shekarun baya.

United ta lashe gasar Firimiya takwas daga cikin 11 a karkashin tsohon kocinta Sir Alex Ferguson, kuma City za ta so ta taka irin wannan rawar a gasar.

Man City ta doke Tottenham da 4-1 ranar Asabar lamarin da ya tsawaita tarihin da suka kafa na nasarorin da suka samu a jere zuwa 16 kuma suka bai wa United da ke binsu a teburin gasar Firimiya ratar maki 11.

Kwantriagin Guardiola zai kare ne a shekarar 2019.

Duka da cewa bai ci wata gasa ba - jagororin City ba su taba tantama kan Guardiola ba

Guardiola,wanda a baya ya yi koci a Barcelona da Bayern Munich ya zama kocin City a lokacin bazarar 2016.

A kakarsa ta farko , kungiyar ta zama ta uku a gasar Firimiya kuma an cire ta a gasar FA a matakin kusa da dab da na karshe kuma ta fice daga gasar zakarun Turai da ta EFL a zagayen kwab daya sili na kungiyoyi 16.

Shugaban kungiyar Khaldoon al-Mubarak ya bayyana kakar a matsayin wata kaka mai yanke buri, amma kungiyar ta yi imanin cewa kocin mai shekara 46 yana cin moriyar aikin da ya yi a wancan lokacin ne a halin yanzu.

Labarai masu alaka