Lanzini na West Ham na fuskantar hukuncin haramcin wasa biyu

Lanzini na faduwa lokacin da Erik Pieters ya nemi kwace bal a wurinsa Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda Lanzini ya fadi lokacin da Erik Pieters ya nemi kwace bal a wurinsa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila (FA) ta tuhumi dan wasan West Ham Manuel Lanzini da laifin yaudarar alkalin wasa ya fadi da gangan aka ba su fanareti a wasansu na ranar Asabar da Stoke City.

Dan wasan dan Argentina ya fadi ne lokacin da dan bayan Stoke Erik Pieters ya tunkare shi domin kwace kwallo, daga nan ne alkalin wasa ya basu fanareti, wadda ta sa suka fara daga raga a wasan da suka yi nasara da 3-0.

An mika batun ne gaban kwamiti mai zaman kansa na musamman na mutum uku wanda hukumar kwallon ta Ingila ta kafa a kan irin laifin , wanda kuma a nazarinsa ya yanke hukuncin cewa dan wasan ya yaudari alkalin wasa ne.

Yanzu an ba wa Lanzini wa'adin har zuwa karfe 6:00 na yamma agogon GMT, ranar Talata, 19 ga watan nan na Disamba ya bayar da bahasi kan tuhumar.

Idan har tuhumar da tabbata wato bai iya kare kansa ba, za a yi masa haramcin wasa biyu, wanda hakan zai hana shi buga wa West Ham, wasan da za ta yi da Arsenal na dab da kusa da karshe na cin kofin Lig, da kuma na Premier a gidansu da Necastle ranar Asabar.

Shi dai kwamitin na musamman na hukumar ta FA, ya kunshi tsohon alkalin wasa daya ne da tsohon kociya daya da kuma tsohon dan wasa daya, kuma har sai dukkaninsu ukun sun amince kafin a aiwatar wa da dan wasan da aka tuhuma da laifi hukuncin hana shi wasa.

Dan wasan gaba na Everton Oumar Niasse shi ne na farko a gasar Premier da aka aiwatar wa da hukuncin hana shi wasan saboda faduwa da gangan ya yaudari alkalin wasa ya ba su fanareti, tun lokacin da aka bullo da dokar a watan Mayu.