Mo Farah ya zama gwarzon wasanni na duniya na BBC na 2017

Gwarzon wasanni na BBC na shekara: Mo Farah Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Na kadu da jin cewa ni na ci kyautar in ji Mo Farah

Zakaran duniya na gudun yada-kanin-wani na mita dubu 10 Sir Mo Farah ya ce ya yi matukar mamaki, kuma ya kasa dena kallon kofin da ya samu bayan an zabe shi a matsayin tauraron wasanni na shekarar nan ta 2017 na BBC.

Farah dan Birtaniya, amma dan asalin Somalia mai shekara 34, kafin bayyana sakamakon masu fashin baki suna ganin shi ne zai yi na uku, amma kuma sai labarin ya sauya ya zama na daya a gaban dan tseren babur Jonathan Rea da dan wasan nakasassu Jonnie Peacock.

Zakaran damben boksin na duniya Anthony Joshua dan Birtaniya wanda shi kuma dan asalin Najeriya ne, shi ake ganin zai zama na daya, amma kuma ya kasance na hudu.

Mohamed Farah wanda ya ci manyan gasa 10 na duniya bai halarci wurin taron bikin bayar da kyautar ba, saboda a daidai lokacin ya dawo Ingila daga Amurka.

Bayan bikin ba da kyautar, a hirar da 'yan jarida suka yi da shi, Farah ya yaba tare da gode wa mutanen da suka zabe shi, yana cewa bashi ne a wurinsa daga jama'ar.