Salah, Mane da Aubameyang na takarar gwarzon Caf

Aubameyang (a hagu) da Mane (a tsakiya) da kuma Salah Hakkin mallakar hoto OTHERS
Image caption A ranar 4 ga watan Janairu Caf za ta bayyana gwarzon na shekara a Accra, Ghana

An zabi dan Masar Mohamed Salah, da na Senegal Sadio Mane da kuma dan Gabon, Pierre Emerick Aubameyang, domin fitar da gwarzon dan kwallon Afirka na bana na Caf a cikinsu.

A makon da ya gabata ne Salah ya zama gwarzon dan kwallon Afrika na BB na wannan shekara, yayin da Aubameyang ya ci kyautar gwarzon Afirkar ta hukumar kwallon kafar ta Afirka, Caf, shekara biyu da ta wuce.

A bangaren mata kuwa 'yar wasan Najeriya Asisat Oshoala, da Thembi Kgatlana ta Afirka ta Kudu da kuma 'yar Kamaru Gabrielle Aboudi Onguene su ne ke gaba wajen samun lambar ta gwarzuwar 'yar kwallon kafar ta Afirka ta CAF.

A fannin lambar gwanin masu horar da 'yan wasa kuwa, kociyan Najeriya Gernot Rohr da Hector Cuper, na Masar tare da kociya Hussein Amoutta na kungiyar Wydad Casablanca, zakarun Afirka su ne ke takara.

A ranar hudu ga watan Janairu na shekara mai kamawa ne za a sanar da wadanda suka yi nasara a Accra bban birnin Ghana.

Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne hukumar kwallon kafar ta Afrika, Caf ta janye kyautar gwarzon dan kwallon Afirka da kke taka leda a gida da kuma ta gwarzon alkalin wasa na shekara, ba tare da ta bayyana dalilin yin hakan ba.