Ina jin dadin aikin horon tuki cikin mayen da aka sa ni - Rooney

Wayne Rooney na isa kotun Majistare ta Stockport Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wayne Rooney a lokacin da ya halarci kotun Majistare ta Stockport yayin yanke masa hukuncin laifin tuki cikin maye

Tshohon kyaftin din Ingila da Manchester United, Wayne Rooney ya ce yana jin dadin aikin da yake yi na hidima a wani lambu na laifin da aka kama shi da shi na tuki cikin maye.

A watan Satumba aka sa dan wasan ya yi aikin sa'a dari na kyauta ba tare da an biya shi ba, a matsayin horo bayan da ya amince cewa ya wuce ka'idar yawan barasar da ya kamata a ce ya sha idan zai tuka mota, linki uku, lokacin da 'yan sanda suka tsayar da shi.

Dan wasan na kungiyar Everton a yanzu wanda a watan Satumbar aka haramta wa tukin mota har tsawon shekara biyu ya ce sakamakon aikin an sa yana jin yadda ake maraba da shi sannan kuma yana jin dadinsa sosai.

Rooney wanda ke daukar albashin fam dubu 150 a sati ya sheda wa kafar watsa labarai ta Talksport, cewa, kai tsaye lokacin da aka tsayar da shi a lokacin bincikin, ya san cewa ya yi shashanci, sai dai kawai ya kori gaba.

Dan wasan wanda ya yi kusan rabin hukuncin, ya ce yana aiki ne da manyan da suke da matsalar koyo a lambun, kuma yana taimaka musu da abubuwa da dama da suke yi a game da bikin kirsimeti.