Alexis Sanchez ya gaji da Arsenal - Ian Wright

Alexis Sanchez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alexis Sanchez ya koma Arsenal ne a shekara ta 2014 a kan kudin da ya kai fam miliyan 35

Dan wasan Arsenal na gaba Alexis Sanchez ba ya kokari kuma yana nuna kamar ya gaji da zama a kungiyar ta Premier in ji tsohon dan wasan Arsenal Ian Wright.

A wata hira da BBC tsohon dan wasan na Arsenal ya ci a yadda Sanchez yake taka leda a yanzu kamar ba ya yi da jikinsa da kuma zuciya daya, ba ya ganin hakan zai yi wa kungiyar wata illa.

Wright, wanda ya ci wa Arsenal kwallo 185 a wasa 288 da ya yi mata, yana ganin dan wasan gaban na Chile yana dagewa a wasansa.

Dan wasan na Chile mai shekara 29 kwallo hudu kawai ya ci a Premier a bana, amma a bara a daidai wannan lokaci yana da 12 ne.

Sanchez, wanda ake maganar cewa zai koma Manchester City a lokacin bazara, kwantiraginsa zai kare a karshen kakar da ake ciki.

Dan wasan ya ci wa Arsenal kwallo 77 tun lokacin da ta dauko shi daga Barcelona a shekara ta 2014.

Wright, wanda shi kuma ya ci wa Arsenal kwallo 185 a wasa 288 da ya yi mata, yana ganin dan wasan gaban na Chile yana dagewa a wasansa.

Ya kara da cewa mutanen da suke son su saye shi , ya za su kalle shi ya za su ga halayyarsa?

Kamar Sanchez, shi ma dan wasan tsakiya Mesut Ozil kwantiraginsa da Arsenal din zai kare a karshen kakar nan.

Dan wasan mai shekara 29 wanda ya ci kwallo daya tilon da Arsenal ta ci a wasan ranar Asabar da ta doke Newcastle, ya taimaka an ci kwallo takwas a bana.

Shi ma dai Ian Wright ba shi da kwarin guiwa dan Jamus din zai tsaya a Arsenal, inda ya kara da cewa za su so a ce yadda yake wasa a yanzu haka yake yi.