Zan iya kociyan kowa ce kungiya a duniya - Moyes

Kociyan WEst Ham David Moyes Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moyes ya jagoranci West Ham ta ci wasanta biyu na karshen nan ciki har da wanda ta doke zakarun Premier Chelsea

Tsohon kociyan Manchester United David Moyes ya ce zai iya horad da kowa ce kungiya a duniyar nan, kuma yana son ya tabbatar da hakan a West Ham.

Ton lokacin da kungiyar ta dauke shi kociya a watan da ya wuce, ta samu fitowa daga rukunin masu faduwa daga gasar Premier, kuma ba a doke ta ba a wasa uku na karshe da ta yi.

Nasarar da ta yi a kan Stoke City da ci 3-0, ta biyo bayan wadda ta doke masu rike da kofi Chelsea da kuma canjaras da Arsenal.

West Ham din ita ce ta 15 a teburin Premier kuma za ta je gidan Arsenal inda za su fafata a wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin lig (EFL), wanda yanzu ake kira Carabao Cup ranar Talata.

Moyes mai shekara 54 yana kokarin dawo da sunansa ne bayan kasawar da ya yi a lokacin da ya jagoranci Manchester United da Real Sociedad da kuma Sunderland.