An kama wani kan zargin nuna wariyar launi ga Raheem Sterling

Raheem Sterling na Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Raheem Sterling ne kan gaba wajen ci wa Manchester City kwallo a kakar nan

'Yan sanda sun kama wani mutum da suke zargi da neman cin mutunci da ma kai hari a kan dan wasan gaba na gefe na Manchester City Raheem Sterling saboda bambancin launin fata.

An bayar da rahoton cewa mutumin ya ci mutunci tare da farma Sterling a lokacin da dan wasan ya je filin kungiyarsu na atisaye a ranar Asabar.

Hukumar 'yan sandan Greater Manchester ta ce sun kama wani mutum mai shekara 29 bisa zargin aikata laifin da ya danganci wariyar launin fata.

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labari kungiyar Manchester City ba ta ce komai ba a kan lamarin.

Babban sufeto mai binciken laifuka na 'yan sandan Paul Walker ya ce ba za a lamunta da nuna wariyar launin fata ba a Greater Manchester, kuma ma abu ne da ba shi da muhalli a cikin duk wata al'umma wayayya. Saboda haka suna daukar duk wani rahoto na irin wannan zargi da matukar muhimmanci.

Raheem Sterling shi ne ya ci kowa cin kwallo a Manchester City zuwa yanzu a kakar nan, inda ya daga raga har sau 15 a dukkanin wasanninta.