'Justin Gatlin na amfani da abubuwan kara kuzari'

Justin Gatlin zakaran tseren duniya dan Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gatlin wanda ya ci lambar gwal a tseren mita 100 na duniya a 2017 bayan da ya doke Christian Coleman da Usain Bolt ya musanta amfani da abubuwan kara kuzari

Zakaran tseren mita 100 na duniya Justin Gatlin ya ce ya kadu tare da mamaki a kan zargin amfani da abubuwan kara kuzari da aka yi wa wakilinsa da kuma kociyansa, wanda ya ce ai dan tseren kamar sauran takwarorinsa a Amurka yana amfani da abubuwan kara kuzari.

Hukumar yaki da amfani da abubuwan kara kuzari a wasanni sun fara gudanar da bincike a kan abin da shugaban hukumar guje-guje ya kira babban zargi a kan Dennis Mitchell da Robert Wagner.

Jaridar Daily Telegraph ta ce Wagner, wanda wakilin Gatlin ne, a boye ya nemi samar da abubuwan kara kuzari ga wasu 'yan jarida da suka batar da kama ko shigar burtu.

Wani hoton bidiyo da jaridar Telegraph ta fitar ya nuna wani mutum wanda jaridar ta ce Wagner ne ke nuna cewa Gatlin yana amfani da abubuwan kara kuzari, shi ma kamar duk wani dan tsere a Amurka.

Jaridar ta kuma ce kociyan Gatlin, wato Dennis Mitchell wanda tsohon zakaran tseren Olympic ne da ya ci lambar gwal, ya gaya wa 'yan jarida, cewa, ba a kama wasu 'yan tseren da suke amfani da abubuwan kara kuzari ne saboda abubuwan da suke amfani da su ba a iya gano su ta gwaji.

Dukkanin mutanen biyu dai sun musanta zargin.

Zakaran tseren na duniya, Ba'amurke Gatlin, mai shekara 35 wanda ya ce ba ya amfani da abubuwan kara kuzari, ya ce yana samun labarin lamarin ya kori kociyan nasa.