Kofin Carabao : Arsenal ta kai wasan kusa da karshe

Welbeck na murnar cin kwallo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A cikin minti na 42 ne Welbeck ya ci wa Arsenal kwallon

Arsenal ta kai wasan kusa da karshe a gasar cin kofin lig (EFL) wanda aka yi wa lakabi da Carabao a bana bayan da Danny Welbeck ya zura kwallo daya tilo a ragar bakin Gunners din West Ham.

Bakin sun dage sosai a fafatawar amma a kusan tafiya hutun rabin lokaci a minti na 42 sai dan wasan gaban na Ingila Welbeck ya keta bayan nasu inda ya ci bal din da Mathieu Debuchy ya dauko masa da ka.

Sai dai Arsenal ta yi asarar dan wasanta Olivier Giroud wanda ya ji rauni a cinyarsa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

To amma duk da haka nasarar ta ba Arsenal damar ci gaba da kasancewa a gasar a karon farko tun shekara ta 1993.