Kofin Carabao :Man City ta kai wasan kusa da karshe bayan doke Leicester

Claudio Bravo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Claudio Bravo ya zama gwanin fanareti ke nan

Manchester City ta tsallake zuwa wasan dab da na karshe na gasar cin kofin lig (EFL) wanda aka sa wa lakabin Carabao a bana bayan da ta fitar da Leicester City a bugun fanareti da ci 4-3.

Bayan da kungiyoyin suka yi gumurzun minti 90 har da karin minti 30 na fitar da gwani suna kunnen doki 1-1, shi ne suka tafi bugun fanareti.

Tun da farko Manchester City ce ta fara daga raga ana minti 26 ta hannun Bernardo Silva, amma kuma bayan minti 90 na wasan an shiga karin lokacin da aka bata, sai Vardy ya farke wa Leicester.

A bugun fanaretin gwanayen 'yan wasan Leicester City biyu Jamie Vardy da Riyad Mahrez su ne suka bara da bugunsu.

Jamie Vardy ya buga ta shi gefe ne ta yi waje, yayin da shi golan Man City Claudio Bravo ya kade ta Mahrez.

Manchester City ta kai wasan kusa da karshe na gasar cin kofin a karo na uku cikin kaka biyar.

A sauran wasannin na dab da kusa da karshe Chelsea za ta karbi bakuncin Bournemouth da karfe 8:45 agogon Najeriya a ranar Laraba

Za a hada jadawalin wasan kusa da karshe ne guda biyu, wato na kungiyoyi hudu bayan an samu sauran kungiyoyi biyu da suka tsallake, inda za a yi wasannin na kusa da karshe gida da waje a watan Janairu.