Madrid na shirin karbar bakuncin Barcelona

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid tana ta hudu a kan teburin La Liga, yayin da Barcelona ke mataki na daya

Real Madrid na shirye shiryen karbar bakuncin Barcelona a gasar La Liga, wasan hamayya da ake yi wa lakabi da El Clasico a ranar Asabar a Santiago Bernebeu.

Madrid wacce ta lashe kofin Zakarun nahiyoyin duniya mai rike da La Liga tana yin atisayen yadda za ta tunkari Barca domin samun nasara idan sun hadu.

Benzema yana daga cikin 'yan kwallon da suke yin atisayen, yayin da Cristiano Ronaldo ya yi nashi shi kadai, shi kuwa Luca a gefen fili ya yi atisayen a kokarin murmurewa da yake son yi daga raunin da ya yi jinya.

Barcelona ce ke mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 42 bayan wasa 16, yayin da Real mai kwantan wasa daya take ta hudu da maki 36.